Mata 'yan Jarida daga jihohi 36 da babban birnin Tarrayya ne kungiyar ta gayyato domin su roki Allah ya kawo karshen tashe tashen hankula da ta'addanci da sauran ayyukan bata-gari da suka addabi al'ummar a Najeriya.
Da take bayyana dalilin kiran wannan taron, shugabar kungiyar ta kasa Madam Ladi Bala, ta ce ganin cewa duk da kokarin da gwamnati ke yi don shawo kan rashin tsaro amma lamarin sai ci gaba da faruwa yake a fadin kasar.
Haka kuma cin zarafi na lalata da sace-sacen mutane don kudin fansa sai kara kazancewa suke yi.
Ita ma Hajiya Rafatu Salami da ta halarci taron addu'o'in har ma ta yi wa'azi a wurin ta ambato wasu matsalolin da ke addabar kasar kamar na cin zarafin mata da yara da sace mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Amma a lokacin da ta ke nazari a wurin taron addu'o'in, shugabar kungiyar mata dattawan Najeriya ta Nigeria Women Elders Council, Madam Chika Ibeneme, ta ce akwai bukatar shugaba Mohammadu Buhari, ya fito ya yi wa kasa bayanin inda matsalar take domin an zubar da jini fiye da kima a kasa,
Chika Ibeneme ta ce mata sun tashi haikan wajen taimaka wa kasar da addu'o'i kuma ta san Allah mai karban addu'arsu ne.
Kungiyar mata ‘yan Jaridu ta Najeriya ta janyo hankalin sauran masu ruwa da tsaki da su kara himmatuwa wajen bada ta su gudumawar wajen fargar da al'umma kan kyautata zamantakewa tsakanin dukkan 'yan kasa ba tare da la'akkari da addini ko jinsi ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5