Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya "MSO" ta yi Babban Taro Mai Taken "Hadin Kan Musulmi da Kalubalen Karni"

wasu mata Musulmi a Najeriya

Shugabar kungiyar ta mata Musulmi Hajiya Salamatu Ibrahim ta ce rabe-raben kan Musulmai yayi yawa a ma duniya baki daya
Kungiyar mata Musulmi ta kasar Najeriya, Muslim Sisters Organization, MSO a takaice, ta yi taron ta na shekara-shekara a Kaduna. Taken taron na bana shi ne "Hadin Kan Musulmi da Kalubalen Karni". Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Isah Lawal Ikara ya halarci taron kuma ya fara ne da tattaunawa da shugabar kungiyar ta kasa Hajiya Salamatu Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Taron Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa a Kaduna - 3:00



Sheikh Ahmed Gummi na cikin manyan masu jawabai a wurin taron kuma ya ce babban kalubalen Musulmi shi ne jahilci, idan da ilimin addini da na duniya babu wata matsala. Ita ma malama Rabi'at Ahmad Sufian shugabar kungiyar tallafwa mata Musulmi a Najeriya ta ce muddin mata suka gyaru to al'umma ta gyaru.