Ranar talatin ga wannan watan Janairu na shekarar 2014 aka tsayar za'a yi zabukan. Shugaban hukumar zabeta jihar Peter Dalyop ya ce kawo yanzu sun tantance 'yan takara daga jam'iyyu shida da suka hada da PDP da APC da APGA da DPP da LP da PDM.
Peter Dalyop ya ce su a shirye suke su gudanar da zabukan na shugabannin hukumomi da kansiloli. Ya ce suna bin tsari daidai babu inda suka kauce ma hanya. Yana fatan haka zasu cigaba har zuwa ranar 30 ga wata da za'a yi zaben.
Dangane da katin zabe Peter Dalyop ya ce aikin INEC ne. Idan mutum ya batar da katinsa to wannan za'a bi dokokin da INEC ta tanada game da hakan. Duk wanda ya rasa katinsa idan ya je wurin INEC zasu fada masa abun da zai yi. Ya kira mutane su fito ilahirinsu da kwansu da kwarkwatarsu su yi zabe cikin lumana da walwala. Kada a yi tashin hankali. Idan akwai wanda bai samu yin zabe ba sai ya yi hakuri ya jira na gaba.
'Yan takara da aka tantance sun ce su basu samu wata matsala ba. Dr. Dung Jeremiah Sale dan takarar neman kujerar shugaban karamar hukumar Barkin Ladi karkashin DPP ya ce yana da tabbaci zasu ci nasara domin kan mage ya waye yanzu ba kamar da ba. Yanzu jama'a basa bin jam'iyya sai wanda ya cancanta. Yawancin 'yan PDP suna yin anfani da matsayinsu na masu rike da gwamnatin jiha ko ta tarayya amma babu abun da suka yi ko zasu yi. Amma ya ce Allah ne mai bada shugabanci. Idan har bai samu ba to Allah ne bai nufeshi da samun ba.
Shi kuma David mai neman shugabancin karamar hukumar Bassa a karkashin PDP ya ce jam'iyyar PDP tamkar tunbin giwa ce. Ya ce babu inda aka yi zabe a duk fadin Najeriya kotu bata kawar da wani daga kan kujerarsa ba sai a jihar Filato.Domin haka idan ana batun kwatanta adalci babu inda ake yin hakan kamar jihar Filato.
Shugaban gamaryar jam'iyyun adawa a jihar Bulus Ibrahim ya ce tun da yawancin jam'iyyu sun sayi takardar zaben nuni ne cewa zasu shiga zaben. Ya ce APC ta je kotu kan zaben amma basu gaya masa ba domin kowa na da nashi ra'ayin.
To sai dai gwamnatin jihar ta Filato ta jinkirta zabe a kananan hukumomin Jos Ta Arewa da Wase bisa ga rahotannin tsaro lamarin da ya sabama tabbacin da kwamishanan yada labarai na jihar Yiljap Abraham cewa za'a gudanar da zabe a duk kananan hukumomi goma sha bakwai na jihar.
Ga karin bayani.