Kungiyar manyan ma'aikatan man fetir a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki

Wani mai zanga zanga dauke da kwalin rubutun adawa a janye rangwamin man fetir

Wata babban kungiyar ma’aikatan man fetir a Najeriya tace zata shiga yajin aiki ranar lahadi idan kasar da tafi kowacce arzikin man fetir a nahiyar Afrika taki maida rangwamin man fetir

Wata babban kungiyar ma’aikatan man fetir a Najeriya tace zata shiga yajin aiki ranar lahadi idan kasar da tafi kowacce arzikin man fetir a nahiyar Afrika taki maida rangwamin man fetir.

Kungiyar ma’aikatan hakar man fetir da iskar gas PENGASSAN ta sanar yau alhamis cewa, zai zama dole ta dauki wannan matakin mai zafi na daina hakar mai idan gwamnati taki sauraronsu.

Najeriya tana fitar da sama da gangar danyen mai miliyan biyu kowacce rana zuwa ketare, kuma daina hakar man zai shafi tattalin arzikin kasar da kuma farashin mai a kasuwannin duniya.

Yau alhamis shugaba Goodluck Jonathan yake ganawa da shugabannin kungiyar Kwadago a gidan shugaban majalisar dattijan kasar.

Idan kungiyar hakar man ta shiga yajin aikin, zata shiga sahun manyan kungiyoyin kwadago biyu da suka kaddamar da yajin aiki ranar Litinin da ya sa dubun dubatar ‘yan Najeriya suka yi zanga zanga da ta gurguntar da harkokin yau da kullum a akasarin manyan biranen kasar.

Aika Sharhinka