Mahalarta taron dai sun fito ne daga jihohin Najeriya 36 da kuma Abuja kuma shugaban kungiyar na kasa Abubakar Balarabe Mahmud, SAN, shi ne jagoran taron.
Batun tsamin dangantaka tsakanin majalisar dokokin Najeriya da gwamnati, da matakin shugaba Buhari na kin nada alkalan kutunan daukaka kara da kuma uwa uba tashin hankulan da ake samu a wasu sassan Najeriya na daga cikin muhimman abubuwan da kungiyar lauyoyin ta zartar da kudiri akan su.
Farfesa Lawan Mamman Yusufari dake zaman tsahon shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Kano kuma shugaban tsangayar nazarin aikin lauya ta jami’ar Bayero Kano ya yi karin haske dangane da kudirorin da suka cimma a yayin taron.
Yace abubuwa da suke faruwa a jihohin kaman su Binuwai, Filato, Nasarawa, Taraba da dai sauransu sun damu kungiyar lauyoyin kasa saboda duk inda aka ce babu zaman lafiya yana shafar rayuwar mutane da ci gaban kasar da ma shari’a kanta.
Kazalika akwai abubuwa da suka yi tsaiko a ayyukan gwamnati irinsu hukumomin da har yanzu ba’a nada masu mutanen da zasu gudanar dasu ba. Ayyukansu sun tsaya. Y ace har ma kungiyarsu ta yi barazanar garzayawa kotu idan nan da wani lokaci ba’a nada jami’an ba. Hatta hukumar saka hannun jari ba’a nada mata mambobinta ba.
Baicin matsalolin da Farfesa Yusufari ya bayyana mahalarta taron sun tattauna dangane da al’amuran da suka shafi hanyoyin inganta aikin lauya a Najeriya da kuma sha’anin babban zaben kasa dake tafe badi.
Barrister Ibrahim Yakubu Umar tsohon atoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, yace maganar kullum itace yaya lauyoyi zasu gyara kasancewar su tsakanin al’umma. Da tabbatar aikin lauya na anfanar jama’ar kasa. Yace akwai bukatar gyara tsarin mulkin kungiyar tasu sannan su dubi irin abubuwan da zasu yi su inganta zaben kasa. Ya kamata kuma a warware matsalar hukumce hukumcen kotuna dake karo da juna.
Taron ya amince da kafa kwamitin zaben shugabannin kungiyar da zai gudana a ranar 27 ga watan Yulin bana a karkashin jagorancin Farfesa Auwalu Yadudu shugaban Jami’ar tarayya dake Kebbi kuma za’ayi zaben ne bisa tsarin sabuwar fasahar zamani mai lakabin E-voting.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5