Gwamnatin jihar Imo karkashin jagorancin Rochas Okorocha, ta kori ma’aikata sama da dubu uku cikin ma’aikatu goma sha tara, hakan ne yasa kungiyar kwadago ta Najeriya sa kafar wando ‘daya da gwamnatin jihar.
A baya dai shugaban kwadago na Najeriya yayi magana baki da baki da Rochas Okorocha, kan wani yunkurin korar ma’aikata a jihar, inda gwamnan ya shugaban kwadago tabbacin ba za a kori ko wanne ma’aikaci ba, sai gashi gwamnan ya karya alkawarinsa.
Majalisar kolin kungiyar kwadago ta bayar da umarnin cewa rundunar kungiyar ta koma birnin Owerri, domin durkusar da duk ayyukan gwamnati baki ‘daya ranar goma ga wannan watan. Hakan ne yasa duk ‘yan kungiyar ke shirye shirye kafin zuwan wannan rana.
Kungiyar kodago bata ganin akwai alamar iya zama a teburi da gwamnan jihar Imo domin sasantawa, kasancewar tana ganin ya yaudareta a baya. Kungiyar dai ta yanke daukar wannan hukunci ne bisa amfani da damar da dokar kasa ta baiwa kungiyar.
Your browser doesn’t support HTML5