Sai dai kuma masana na ganin akwai abin dubawa ga kalaman shugaban Najeriyan, ‘daya daga cikin shugabannin kungiyar lauyoyin jihar Taraba barista Idris Abdullahi Jalo, yace akwai alamar karatun ta nutsu ga wannan kalami na shugaban kasa.
Barista Idris yace shi a fahimtarsa ba wai shugaban kasa yana zargin alkalan kotu da kin bashi hadin kai wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, abin nufi anan shine dokar kasa ta tanadar idan ana tuhumar wani da aikata kowanne irin laifi, to dole sai gabatar da shi gaban kuliya a kuma bashi hakkin kai na kare hakkin kansa. Kafin kotu tayi nazarin yanke masa hukunci.
To sai dai kuma ga ‘yan rajin kare hakkin ‘Dan Adam irin su Mallam Musa Jika, ya danganta wannan tafiyar hawainiyar ne da shakulatin bangaro da ga bangaren masu shigar da kara. Inda yake cewa bai kamata ba a daurawa alkalai laifin cewa sune ke kawo jinkiri akan maganar shari’u. ya kuma nemi gwamnati da ta sake duba tsarin da zata taimakawa lauyoyi don tabbatar da sunyi aikin su yadda ya kamata.
Shugaba Buhari ne dai ya koka kan yadda yake ganin alkalai kan iya kasancewa babbar barazana ga cimma burin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.