Kungiyar Kiristocin Najeriya Reshen Borno Na Fatan Batun Sulhu da Boko Haram Gaskiya ne

Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima

Sabili da yadda kungiyar Boko Haram ta sha karyata batun yin sulhu da ita can baya yasa wasu da dama na tababan batun tsagaita wuta da aka ce an cimma domin har yanzu ana samun hare-hare a jihohin Borno da Adamawa.

A nata martanin akan batun sulhu kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Borno tace Alla yasa batun ya zama gaskiya ne ba yaudara ba ce kamar yadda aka saba gani.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani fira da tayi da Muryar Amurka a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno. Shugaban kungiyar Rabaran Fona yace bukatarsu ita ce wannan shirn tsagaita wuta da gwamnati da 'yan Boko Harama aka ce suna yi a kasar Chadi ya zama gaskiya ba yaudara ba. Yace an sha yin irin wannan shirin amma daga baya sai a gane ba gakiya ba ne.

Fatan kungiyar shi ne su 'yan Boko Haram su amince su sako duk mutanen da suke garkuwa dasu, wato 'yan matan Chibok da sauran matan dake hannunsu. Shi Rabaran Fona dan asalin garin Chibok ne.

Yace akwai 'yan matan Chibok fiye da dari biyu a hannun 'yan Boko Haram. Akwai wasu matan da kungiyar ke rike dasu. Tunda suka yi alkawarin yin yarjejeniyar sakin 'yan matan to Allah yasa hakan ya tabbata.

A wani hannu kuma uwar jam'iyyar APC ta kasa tace tana da ja da batun sulhun da gwamnatin tarayya da 'yan Boko Haram. Alhaji Dikko Umaru wakilin jam'iyyar na kasa yace sanarwar da gwamnati tayi siyasa ce kawai domin bayan sun sanarda tsagaita wuta ana cigaba da kashe mutane a jihar Borno. Yace sun kawo maganar ce domin su yaudari mutane su samu ci zabe mai zuwa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Kiristocin Najeriya Reshen Borno Na Fatan Batun Sulhu da Boko Haram Gaskiya ne - 3' 55"