A cikin sabon makon nan ne ake sa ran gwamnatin Najeriya da kungiyar Boko Haram zasu yi shawarwari kan sharuddan sakin ‘yan matan nan ‘yan makaranta su fiyeda metan, da ‘yan kunigyar suka kama suke garkuwa da su tun cikin watan Afrilun bana.
A ranar jumma’a sassan biyu suka amince da shirin tsagaita wutar.Kuma ana sa ran ci gaba da shawarwari tsakanin duka sassan biyu gobe litinin a cadi.
Zuwa yanzu dai Boko Haram bata fito fili tace kala ba kan wannan yarjejeniya da aka ce an kulla.
Rahotannin da suke cewa an kai sabbin hare hare kan wasu kauyuka ranar jumma’a da kuma Asabar, yasa an fara rade raden cewa kungiyar tuni ta keta yarjejeniyar. Amma gwamnatin Najeriya tace ba’a keta yarjejneyar tsagaita wutar da aka kulla ba.
Wani babban hadimin shugaba Goodluck Jonathan Doyin okupe, ya gayawa MA cewa shugabannin kunigar BH sun amince da yarjejnieyar, sannan tashe tashen hankulan wasu tsiraru ne cikin kungiyar wadanda har yanzu sai tayu basu sami labarin an kulla yarjejeniyar ba.
Wani wakilin MA yace an kashe akalla mutane 40 a sabbin hare haren da aka kai kan wasu kauyuka a jihar Barno.