Kungiyar iyaye da malaman ta kasa dai ta ce maganar matsalar tsaro ta riga ta ta'azzara saboda haka ya kamata gwamnati ta bude wa iyayen yara kofa su ma su bada ta su irin gudummawar, kamar dai yadda shugaban kungiyar na kasa, Alh. Haruna Danjuma ya bada shawara.
“Danjuma ya ce idan gwamnati ta amince, kungiyarsu za ta rinka karbar kudi daga hannun iyayen daliban don biyan mafarautan da za su kare makarantun Najeriya saboda aikin ya fi karfin jami'an tsaro su kadai”.
Sai dai ganin makaman da ke hannun 'yan-bindiga da sauran 'yan-ta'adda ya sa wasu tunanin cewa kungiyar mafarauta ba za ta iya tunkarar matsalar tsaron da ke barazana ga makarantu ba. Amma shugaban kungiyar na jahar Kaduna, Malam Ibrahim Datti ya ce kungiyar ta wuce yadda wasu ke tunani.
Karo-karon kudin don kula da makarantu dai ka iya zama kalubale musamman ganin duk lokacin da aka koma makaranta dai iyaye kan fuskanci hidimomin kashe kudi. Shi yasa ma wasu iyayen su ka ce ko da an ce a kawo kudi, ba za su iya ba.
Dama dai ganin matsalar tsaro ya sa gwamnatin jahar Kaduna bada umarnin kafa kwamitin tsaro a dukkan makarantu don taimaka wa jami'an tsaro wajen magance matsalar baki daya.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5