Kungiyar ISIS Nada Mayaka Fiye da Dubu Talatin

Mata mayakan ISIS

Hukumomin leken asirin Amurka sun tabbatar cewa kungiyar ISIS nada mayaka fiye da adadin da ake zato kuma nasarorin da ta samu har ta kafa daula sun sa sabbin mayaka na kwarara zuwa yankin.

Hukumomin leken asirin Amurka sun ce kungiyar mayakan sakai da ake kira ISIS tana da mayaka da suka kama daga dubu 20-zuwa sama da dubu talatin.

Kakakin hukumar leken asiri ta Amurka ya fada jiya Alhamis wannan kiyasi ya saura sosai sama da kiyasin dakaru dubu da aka yi a baya.

Yace sabon alkaluman ya nuna karfin ci gaba da kungiyar ta samu na daukan sabbin mayaka tun cikin watan Yuni bayan nasarori da kungiyar ta samu a faggen yaki da kuma ayyana daula data yi a yankunan Iraqi da Syria.

Tunda farko ministoci 10 daga kasashen Larabawa da suke yankin Gulf sun ce sun dukufa wajen aiki tareda da Amurka wajen wargaza kungiyar ISIS ko da a ina take, har a cikin kasashen Iraqi da Syria.

Jami’ai daga kungiyar hadakan kasashe dake yankin na Gulf tareda Masar da Iraqi da Jordan da kuma Lebanon sun ce du kawunansu na hade wajen yin adawa da ta’addanci ko da a ina ne.

Ahalinda ake ciki kuma, kawayen Amurka a turai bakunansu basu daidaitu ba kan ko zasu shiga sahu da Amurka wajen kai farmaki da jiragen yaki a Syria. Tuni dai Amurka ta kai hare hare ta sama har sau 150 kan wurare da masu tsatsauran ra’ayi suke rike dasu a Iraqi, suka fatattake su.