Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Kai Wasu Hare Hare Da Kisan Dakarun Nijar

Reshen kungiyar IS a Yankin Sahara ya dauki alhakin kai wani hari da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin jamhuriyar Nijar sama da 80 a makon jiya a barikin Chinagoder da ke bakin iyakar Nijar da Mali.

Wasu masu sharhi akan harkokin tsaro na ganin wannan a matsayin wani bangare na wata ajanda da kungiyar ta tsara don cimma wani buri a shekarar nan ta 2020.

Wannan shine karo na biyu da reshen na IS a yankin Sahara ke daukar alhakin kai munanan hare haren da su ka yi sanadiyar mutuwar sojojin Nijar kusan 200 cikin wata daya duk akan iyakar kasar da Mali.

Kamar yadda abin ya wakana a washe garin harin barikin Inates, a wannan karon ma kungiyar ta’addancin ta yi amfani da kafafen sada zumunta don yada bayanan abubuwan da suka faru a barikin Chinagoder a ranar alhamis 9 ga watan Janairun da ya gabata.

Sanarwar kungiyar wacce aka yada da kuma wasu hotuna da ake dangantawa da harin na Chinagoder, ta ce mayakan reshen IS a yankin Sahara sun yi nasarar kashe sojoji 114.

"Shugaban reshen kungiyar ta IS a yankin Sahara, Adnan Abu Walid Al Sahrawi, ya sami karfin zama sosai a Arewacin Mali, abin da ya baiwa shugabannin kungiyar damar samun magoya baya daga cikin al’umma sakamakon rashin samun kulawar da ta dace daga wajen hukumomi," a cewar Abdou Idi na kungiyar rajin kare demokradiyya ta FSCN.

A wani abinda ya zama bakon al’amari, wasu rokokin da ba a san daga inda aka harbo su ba sun fadi a jiya da asuba a kauyen Kongou da ke gabashin birnin Yamai, kuma a cewar wasu bayanai abin na da nasaba da ayyukan ta’addanci.

A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Kai Wasu Hare Hare Da Kisan Dakarun Nijar