Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Harin Gidan Rawar Turkiyya

Hotunan mutanen da suka mutu a harin gidan rawa a Turkiyya

A yau Litinin kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a ranar da sabuwar shekara ta kama a wani gidan rawa a birnin Istanbul dake Turkiyya.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna cewa wasu “sojan daularta” ne ya kai harin bindigar.

Kafofin yada labaran kasar ta Turkiyya a yau Litinin sun ruwaito cewa an kama mutum takwas da ake zargin na da hanu a harin, amma kuma babu dan bindigar a cikinsu.

A dai ranar Lahadin da ta gabata dan bindigar ya harbe mutane akalla 39 cikin har da wani dan sanda a wani gidan rawa mai suna Reina kafin ya arce.

Akwai akalla mutane 600 ke cikin gidan shakatarwan, kuma daga cikinsun sai da suka fada cikin Mishigin tekun Bosporus kafin su tsira da ransu.

A wata sanarwa da ya fitar shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kwatanta wannan hari a matsayin “hari na rashin Imani.”

Wani kakakin sabon sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Anotnio Gueterres ya yi Allah wadai tare da yin fatan za a za a kama wadanda ke da hanu a harin.