Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Yana Tababan Shigshigin Rasha A Zaben Amurka


Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado
Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado

Jami’an Amirka sun ce basu da bayanin cewa anyi satar shiga kamfanin bada wutar lantarki a jihar Vermont dake arewa maso gabashin Amirka, a yayinda suke ci gaba da binciken wata na’urar satar bayanai da aka samu cikin injin mai kwakwalwa irin wanda ake rikewa.

Ma’aikatar tsaron cikin gidan Amirka ta fada a ranar Asabar da dare cewa an hada injin mai kwakwalwa din da wayar wutar lantarkin kamfanin Burlinghton. Nan da nan ma’aikatar tsaron cikin gidan ta dauki matakin raba injin din da wayar wutar lantarkin.

Gano wannan abu yasa Amirka ta nuna damuwa akan yadda za’a iya satar shiga wani kamfani da masana’antar kasar.

Matsalar da aka samu a jihar Vermont tasa jihohin Amirka damasuka fara binciken ko ana satar shiga kamfanonin su ko masana’antun su.

To amma shugaban Amirka mai jiran gadon Donald Trump yana ci gaba da tababar ikirarin da hukumar leken asirin Amika ta yi cewa kasar Rasha tayi shishigi a zaben shugaban Amirka ta hanyar satar shiga injin mai kwakwalwa.

Wannan al’amari da hukumar leken asirin Amika ta gano, yasa shugaba Barack Obama ya bukaci a azawa hukumomin leken asirin Rasha takunkunmin da kuma korar wasu ma’aikatan jakadancin Rasha talatin da biyar bisa zargin cewa ‘yan leken asiri ne

A jajibirin shiga sabuwar shekara Donald Trump ya fadawa yan jarida a gidansa dake jihar Florida cewa yana son a tabbatar da kafofin hukumar leken asirin Amirka kafin a dauki wani mataki.

Yace ba za’a yiwa Rasha adalci ba idan aka dauki wani mataki ba tare da tabbatar da gaskiyar abinda ya faru ba.

XS
SM
MD
LG