Kungiyar HCNE ta yi kira da babbar murya ga ECOWAS ta dubi halin da al’ummar Nijar ke ciki da idon basira, don samar da sauki ga yanayin da al’ummar kasar ke ciki.
Wakilan kungiyar HCNE reshen Najeriya, karkashin sabon shugaban ta Alhaji Ahmadu Tasi’u Kalgo, sun bayyana wa manema labarai a Abuja, cewa akwai damuwa sosai kan takunkunmin da ECOWAS ta kakaba wa Kasar Nijar, lamarin da ya shafi alumma ta fannoni rayuwa da zamantakewa.
Tasi'u ya ce kungiyar HCNE ta na kira da babbar murya ga kungiyar ECOWAS ta janye takunkumin da ta kakaba wa Nijar, domin al'umomin Nijer suna shan wahala sosai.
Kungiyar ta ce ba takunkumin shige da fice kadai ne ba, akwai na kudade da kasashe masu amfani da kudin CEFA wadanda aka fi sani da UEMOA suka dora wa kasar Nijar, wani nau'i na takunkunmin cire kudade a asusun ajiya a Bankuna.
Sakataren kungiyar HCNE Abubakar Namata, ya yi godiya da hadin kan da 'yan Najeriya suka nuna wa al’ummar Nijar, tare da shan alwashin aiki tukuru wajen farfado da kungiyar.
Masanin harkokin siyasa da diflomasiyya na kasa da kasa, kuma malami a Jami'ar Abuja, Dokta Abu Hamisu, ya yaba da yunkurin kungiyar na yin kiraye-kiraye, wanda ya ce na iya yin tasiri a wani bangare.
Hamisu ya ce shugabanin ECOWAS suna da masu gidajen su daga kasashen Turai, wandanda su ke ba su umurni, saboda haka zai yi wuya a samu yadda ake so cikin sauki.
Abin jira a gani shi ne ko shugabanin sojin na Nijar za su bi umurnin kungiyar ECOWAS, wajen sako tsohon shugaban kasar Mohammed Bazoum, a bisa sharadi na janye takunkumi.
Your browser doesn’t support HTML5
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.