Hadaddiyar kungiyar CODEO dake saka ido kan harkokin zaben kasar Ghana, domin neman kiyaye da kuma hana magudi. Kungiyar dai na amfani da wani sabon salon kidayar zaben wanda zai bayar da damar gano yadda zaben zai kasance kafin a kammala.
A wata tattaunawa da yayi da Muryar Amurka babban jami’in kungiyar CODEO Sheikh Armiyau Shuaibu, yace idan har suka sami banbancin sakamakon zabe da wanda hukumar zaben Ghana ta fitar, kungiyar zata nemi zama da shugabar hukumar zabe domin kwatanta sakamakon zaben biyu da kuma fahimtar juna.
Akwai wasu jam’iyyu a Ghana dake ikirarin cewa zasu ambata nasu sakamakon zaben, sai dai Sheikh Armiyau Shuaibu yace wannan ya sabawa dokar kasa, kuma hukumar zabe ce kawai take da ikon ambata sakamakon zaben da akeyi.
Domin karin bayani saurari hira da Sheikh Armiyau Shuaibu shugaban kungiyar CODEO mai sa ido a zaben Ghana.
Your browser doesn’t support HTML5