Kungiyar daliban Hausa ta Najeriya da hadin gwiwar sashen koyar da harshen Hausa sun gudanar da taron ranar harshen Hausa na wannan shekara.
Aliyu Muhammadu Bunza, malami ne a jami’ar tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, haka kuma malami ne a jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto, wanda ya gabatar da mukala mai taken ‘Hausa da Hausawa’ wanda ya ce harshen Hausa lallai ya ciri tuta domin kuwa har yanzu harshen yana da tasiri a duniya.
Sannan ya kara da cewa duk yawancin harsuna akan aro wata kalma daga wasu harsuna, wanda hakan na faruwa ne sakamakon cudanya ta cinikayya da aurataiya da ya shiga tsakani.
Farfesa Bunza, ya ce hanya daya da za a kara bunkasa harshe, ita ce ta hanyar amfani da harshen uwa wajen koyar da darussa da wasu ayyukan ci gaba.
Kwamred Nura Suleman Jar birji, sabon sarkin daliban Hausa na kasa, ya ce wannan shine karo na farko da aka fara gudanar da wannan taro na ranar Hausa, wanda ya ce sun gudanar da taron ne domin nuna muhimmancin harshen Hausa tare da nuni da cewar a duk fadin nahiyar Afrika babu wani harshe da yake kamar harshen Hausa.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5