Sakar itacen kaba wata dadaddiyar sana’a ce a Najeriya amma bukatar kayayyakin kasashen waje a Najeriya sun janyo durkushewar wannan sana’ar, kuma mutane da yawa dake yin ta na gwagwarmaya wajen samun na kashewa. Ko da yake, wata dokar gwamnati da ta hana shigowa da kayan kasashen waje ta fara habbaka sana’ar ta kayayyakin na sakar kaba a Najeriya. Wasu ‘yan Najeriya na ci gaba da rike wannan sana’ar.
Kama daga yankan itacen zuwa sarrafa shi da kuma saka shi, Sunny Anegbbode ya kan bi yayan shi wurin wannan sana’ar sama da shekaru 20 da suka wuce.
Sakar itacen kaba na zaman wani bangaren al’adar al’ummar yankin jihar Edo dake kudancin Najeriya.
Amma Anegbode dake zama a babban birnin tarayyar Abuja, yana fatan bunkasa sana’arsa.
Ya ce ya fara wannan sana’ar ne a lokacin da yake makarantar firamare, ya na dan tabawa kadan-kadan kafin ya kware a sana’ar.
Itacen kaba, da yake yana da taushi, ana amfani da shi wajen saka kwando, ko kujeru, da ma soron gini.
Da yake kokawa akan kalubalen da suke fuskanta a sana'ar, Sunny Anegbode ya ce “ko ya ka sarrafa kayayyakin kaba, jama’a zasu ce ai a gargajiyance aka yi su, ko da ya yi su kamar na kasashen waje. Dalili kuwa shine jama’ar kasar su na da dama da hanyar sayen na wajen kuma da yadda ‘yan Najeriya ke tunani, saboda wasu sun yi imanin cewa duk abin da ya fito daga waje ya fi wanda aka yi a gida Najeriya.
Amma a wannan shekarar gwamnatin Najeriya ta fidda dokar hana shigo da kayayyakin kasashen waje, ciki har da kayayyakin da aka sarrafa da katako. Gwamnatin ta ce ta na so ta inganta wannan bangaren a kasar.
A yayin da masu sakar kaba ke fatan ganin wannan doka ta taimakawa sana’o’insu, masu harkar aikin kafinta kamar Emmanuel Onwe na daukar matakai na kokarin bude masana’antar kaba a gefe guda.
Facebook Forum