Bidiyon, wanda ya bayyana a kafar yada labaran az-Zallaqa a daren Juma'a, ya nuna wasu mutane biyu da suka ce mayakan sun kama su a lokacin da suke aiki a Baga da ke arewa maso gabashin Nijar.
Mazan guda biyu, sun yi magana a cikin a bidiyon. Daya daga cikinsu ya bayyana kansa a matsayin Yury, yana mai cewa shi masanin ilimin yanayin kasa ne kuma yana aiki da wani kamfanin kasar Rasha a lokacin da ‘yan mayakan kungiyar JNIM masu alaka da al-Qaida a yankin suka kama shi. Dayan mutumin shi ma ya bayyana sunansa, amma ba iya jin shi ba sosai, ya ce ya yi wata guda a Nijar.
Kamfanin dillancin labaran AP bai iya tantance sahihancin bidiyon ba da kuma lokacin da aka dauke shi. Mutanen da suka yi magana da harshen turanci, ba su bayyana lokacin da aka kama su ba.
Wata majiyar tsaro a Nijar da ta nemi a sakaya ta, ta ce kusan mako guda kenan da aka sace mutanen biyu a yayin da suka kai ziyara wata mahakar zinare.
Wannan ne karon farko da aka ga mutanen. Idan zancen ya tabbata, to sun zama 'yan Rasha na farko da mayakan jihadi suka yi garkuwa da su a yankin Sahel, duk da kasancewar sojojin Rasha a yankin.
Yayin da dangantaka tsakanin kasashen yammacin duniya da kasashen da sojoji suka yi juyin mulki a yankin kudu da hamadar Sahara ke tabarbarewa, Rasha na amfani da wannan damar ta tura mayakanta da kuma karfafa tasirinta a yankin.
A 'yan watannin baya-bayan nan Nijar ta janye daga abokan huldarta na yammacin duniya musamman Faransa da Amurka, a maimakon su ta rungumi Rasha domin samar da tsaro. A cikin watan Afrilu, masu horar da sojoji na Rasha suka isa Nijar don karfafa matakan tsaron Nijar ta sama.
Wannan bidiyon dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da kungiyar al-Qaida ta yi ikirarin kai hari mafi muni kan sojojin hayar kungiyar Wagner na Rasha a shekarun baya-bayan nan, a lokacin da ta yi wa mayakan kwantan bauna a Mali har ta kashe sojoji 50.
Nan take dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha ba ta mayar da martani ba game da mutanen da aka yi garkuwa da su.