Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Faransa Sun Kammala Ficewa Daga Kasar Nijar


Dakarun Faransa a Jamhuriyar Nijar.
Dakarun Faransa a Jamhuriyar Nijar.

Kasar Faransa ta kammala janye sojojinta ranar Juma’a bayan da sabuwar gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta bukaci su fice daga kasar.

Lamarin janyewar dai ya kawo karshen tallafin soji da Faransa ta kwashe shekaru ta na yi, tare da nuna damuwa daga manazarta dangane da gibin da ake samu a yakin da ake da mayakan yan ta’adda a yankin Sahel na Afirka.

Jiragen saman sojojin Faransa na karshe sun bar Nijar a ranar 22 ga watan Disamba, wa’adin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta kayyade, bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli, kamar yadda babban hafsan sojin Faransa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press ta kafar sakon email. Tuni Faransa ta sanar a wannan makon cewa za ta rufe ofishin diflomasiyyarta a Nijar har na tsawon wani lokaci.

Duk da haka, kasar za ta ci gaba da shiga cikin yankin Sahel, da ke kudu da hamadar Sahara wanda ya kasance wuri mai zafi ga masu tsattsauran ra'ayi - ko da yake ya sha bamban, in ji shugaba Emmanuel Macron a ranar Alhamis yayin wata ziyara da ya kai wani sansani a Jordan.

"Na yanke shawarar wasu muhimman sake fasalin," in ji Macron. "Za mu ci gaba da kare muradunmu a can, amma sojojinmu ba za su kasance a can har dindindin ba, za su kasance masu zaman kansu," in ji shi.

Majalisar mulkin Nijar ta bayyana kawo karshen hadin gwiwar soji da Faransa a matsayin mafarin sabon zamani ga 'yan Nijar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG