A taron manema labarai da kungiyar BBOG ta kira a daidai kofar shiga fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock, tsohuwar ministar ilimi kuma jagorar kungiyar Obi Ezekwesili ta ce kungiyar zata canza salonta.
Manufar canza salon domin ta kalubalanci gwamnati ne wajjen ganin an kwato sauran 'yan matan cikin sauri.
Inji Obi Ezekwesili "muna cikin fushi da juyayi yadda gwamnati ta yi sakaci aka sake maimaita abun da ya faru a Chibok shekaru hudu da suka gabata. Yanzu haka an sake sace 'yan mata 110 a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya"
A lokacin da take ci gaba da bayani, Obi Ezekwesili ta yiwasu tambayoyi guda goma sha hudu dake bukatar amsoshi daga bangaren gwamnati.
Edith Yasin jigo a kungiyar ta yi karin haske akan batun. Ta ce duk tambayoyin da aka yi gwamnati ta yiwa Allah ta bada amsoshinsu. Idan kuma ba'a bada amsoshin ba ke nan babu abun da ake yi akan 'yan matan da aka sace.
Shi ma babban lauyan kasa Femi Falana ya yi karin haske akan hurumin da kundun tsarin mulki ya ba gwamnati.Hakkin gwamnati ne ta kare lafiya da dukiyoyin duk 'yan Najeriya.
Kungiyar ta ce nan da mako daya idan bata samu amsoshin tambayoyin da ta mika ba, zata shigar da kara a kotu.
Medina Dauda nada karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5