NIANEY, NIGER - A rahoton da ta fitar a ranar Litinin 21 ga watan nan na Maris kungiyar Amnesty International ta gargadi hukumomin Nijar da su dauki matakan mutunta ‘yancin fursunoni a gidan yarin Koutoukale inda bayanai ke nunin ana toye ‘yancin samun ziyara wanda hatta lauyoyin dake kare ‘yan kaso ba sa samun damar ganawa da mutanensu.
Sannan ‘yan kaso ba sa samun ganin likita domin duba lafiyarsu kamar yadda ya dace.
Kungiyar ta yi tur da abinda ta kira hana shiga kurkukun Koutoukale da abinci ko ruwan sha ko wasu abubuwan bukatan fursunoni daga waje, lamarin da ta ce ya saba wa dokokin kasa da kasa.
Da yake bayyana ra’ayinsa dangane da korafin na Amnesty International shugaban kungiyar AEC Moussa Tchangari ya ce shi ganau ne a game da yanayin da fursunoni ke tsare a gidajen yarin Nijer.
A nata bangaren, hukumar kare hakkin dan adam ta kasa CNDH tace tuni ta tattauna wannan batu da gwamnatin kasar wace ta yi alkawarin daidaita al’amura cikin gaugawa.
Hukumar tace la’akari da matsalolin da ‘yan kaso ke fama da su a gidajen yari da dama cikinsu har da na Koutoukale ya sa ta ja hankulan mahukunta a yayin wata ganawar shugabaninta da Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou a farkon watan nan da muke ciki kamar yadda kakakin hukumar Insa Garba ya shida mana.
Gidan yarin Koutoukale dake a km 50 a kudu maso Yammacin birnin Yamai na daga cikin kurkuku mafi tsaurara matakan tsaro a nan Nijar, lamarin da ya sa hukumomi ke ajiye gaggan ‘yan ta’adda da manyan ‘yan ta kife a cikinsa.
A shekarar 2016 wasu ‘yan bindiga da aka bayyana a matsayin mayakan kungiyar IS sun kai hari da nufin fitar da mutanensu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5