Kungiyar Al Shabab ta Kashe Mutane 28 a Kasar Kenya a Yau Asabar

Wasu dakarun al-Shabab.

'Yan sanda a arewa mso gabashin kasar Kenya sunce wasu 'yan bindiga yan kungiyar Al Shabab sunyi wa wata motar fasinja kwantar bauna suka kashe mutane ashirin da takwas wadanda ba Musulmi ne ba, aka ware su daga cikin fasinjoji sittin.

Kungiyar Al Shabab ta Somaliya tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin, tana mai fadin cewa ramuwar gaiya ce ga sumamen da jami'an tsaron kasar Kenya suka kai wani Masalaci a birnin Mombasa.

Hukumomi sun ce yau Asabar yan yakin sa kan suka kaiwa bas din hari, a kimamin kilomita hamsin daga birnin Mandera kusa da kan iyakar kasar Kenya da Somaliya.

Tun dai lokacinda kasar Kenya ta tura sojojinta zuwa Somaliya a shekara ta dubu biyu da goma sha daya take fama da hare hare da tashin bama bamai da aka dora alhakinsu akan kungiyar Al Qaida wadda take da alaka da yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab ta Somaliya.

Sojojin Kenya suna cikin sojoji kungiyar kasashen Afrka da aka tura Somaliya domin su taimakawa gwamnatin Somaliya wadda bata da karfi sosai daga tawayen kungiyar Al Shabab