Kungiyar al-shabab ta mayakan sakai a kasar Somaliya ta dauki alhakin kashe wakili na biyu dan majalisar dokokin kasar kwana daya bayan da suka halaka wani takwaran aikinsa.
Kungiyar ta al-shabab tace ta harbe Abdiaziz Isaq Mursal, wanda ya mutu jiya talata, bayan wani kwanton bauna da ‘yan binidgan suka yi masa a gundumar Dharkaynley dake birnin Mugadishu.
Hukumomin kasar sun ce anyi ta harbinsa kuma nan take ya mutu.
Ranar litinin kungiyar mai alaka da kungiyar al-Qaida ta dauki alhakin kashe dan majalisa Isak Mohammed Ibrahim ta hayar dana bam cikin motarsa, harin ya kuma raunana wani dan majalisa.
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Somalia, Nicholas kay, yace hare haren suna kara yin tunin cewa, duk da cewa kungiyar mai ikirarin bin tafarkin addinin Islama ta yi hasarar yankunan data mamaye cikin ‘yan shekaru da suka wuce, har yanzu tana ci gaba da zama barazana ga kasar.