A baya bayan nan wani magidanci mai suna Mallam Muhammad, ya arce biyo bayan haifa masa yan uku da mai dakinsa ta yi, da yanzu haka take kwance a babban asibitin kwararru da yaran da ta haifa cikin mawuyacin hali.
Malama Maryam itace matar data haihu, ta kuma bayyanawa wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz halin da suke ciki a yanzu ita da jarirai Ukun data haifa. tace “Na gode Allah, wannan shine haihuwata na Uku, domin ina da yara Hudu, kuma tun lokacin da nazo awo bayan da likitoci suka duba ni, suka yi hasashen cewa zan haifi yan Uku, wato lokacin cikin na wata Bakwai tun a wannan lokacin ne naga kamar hankalin mai gidana ya tashi, yakuma soma kokawa. Yanzu ga shi baya nan, kuma ina cikin wani hali, ga rashin abinci mai gina jiki, ga ba wani abun da zan basu. Gaskiya ina son a taimaka min.”
Ta ci gaba da cewa kullum aka bugawa mijinta waya sai yace gashin nan zuwa, amma yanzu kusan mako guda bashi ba labarinsa.
Yanzu haka likitoci da kuma jami’an asibitin ne ke taimakawa Maryam wajen kula da wadannan jarirai. Mrs Selivie Ahmad Danaba, na daga cikin jami’an dake tallafawa Maryam, tace ba kasafai ake samun irin wannan haihuwa ba ta ‘yan Uku, wanda baifi a samu sau Daya ko Biyu ba idan anyi sa’a sau Uku a shekara.
To sai dai yayin da Maryam ke kokawa ita kuwa Madam Patience David, da ita ma ta samu irin wannan karuwa ta ‘yan Uku makonni Biyu da suka gabata, tace tabbas haihuwar ‘yan Uku akwai wahala, idan aka hada da yadda kaya sukayi tashin gwauran zabi kuma babu kudi da za ayi dawainiyar yaran.
Muryar Amurka tayi kokarin jin ta bakin kwamishinan harkokin mata da walwalar jama’a na jihar Adamawa Alhaji Aliyu Tola, to amma haka ta bata cimma ruwa ba.
A Najeriya da wasu sassa da dama na kasashen Afrika, kuncin rayuwar da jama'a ke fama da shi a sakamakon matsalar tattalin arziki, matsala ce da kusan ta zama tsumagiyar kan hanya - fyadi yaro - fyadi - babba.
Saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz daga Yola.
Your browser doesn’t support HTML5