Rundanar sojan tace tana nan tana gudanar da bincike don ci gaba da gano irin wadannan mutane dake da hannu wajen sace Shanun makiyaya. Yawanci dai kungiyoyin makiyaya suna kokawa kan yadda ake farwa Fulani a daji lokacin da suke kiwo a kashe su a kuma kwashe musu Shanunsu.
Kwamandan rundunar sojan Najeriya shiyya ta 7 dake garin Maiduguri Majo Janal Lucky Irabor, yace sun riga sun kame wadannan mutane kuma suna nan suna ci gaba dagudanar da bincike a kansu, wanda daga bisani zasu bayyanawa manema labaru duk abin da suka gano.
Janal Irabor, ya karyata zargin da ake na cewa jami’an soja na karbar na Goro idan zasu raka wasu motoci zuwa garin Gamboru, wanda yace ba haka bane domin sojoji basa bukatar taimako daga kowacce kungiya.
Shugaban kungiyar masu motocin sufuri na jihar Borno, Alhaji Bello Madaganari, yace yanzu haka an fara jigilar dukkannin fasinjojin da suka yi zanga zanga a karshen makon da ya gabata, na cewa rundunar sojan tayi watsi da su tana kai wasu motoci ne kawai.
Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda.