Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Man Fetur Na NNPC Ya Musanta Raderadin Kara Farashin Mai


A duk lokacin da aka fara raderadin kara farashin mai sai an samu layin ababen hawa a gidajen mai na kasar
A duk lokacin da aka fara raderadin kara farashin mai sai an samu layin ababen hawa a gidajen mai na kasar

Tun ba yau ba ake ta kai da kawowa akan batun karin farashin litar man fetur a Najeriya, kuma kowane lokaci kamfanin NNPC yace babu niyyar a kara, su ma masu shigo da mai dake zaman kansu su ce babu gaskiya a batun karin

Kamfanin ya musanta kara farashin man fetur daga lita dari da arba'in da biyar akan kowace lita daya.

A wani taro a Legas cibiyar kasuwancin kasar, daraktan sashin gurbataccen mai na kamfanin Mr. Kyari yace kamfanin ba zai iya cigaba da sayar da mai akan nera 145 kan kowacce lita daya ba domin hakan na tarawa kamfanin bashi.

Jami'in labarun kamfanin Garba Deen Muhammad yace ba'a fahimci abun da Kyari ke nufi ba ne. Yace sam babu batun sauya farashin litar.

Yace daraktan yana bayar da dalilan da masu dakon mai suke akan batun karin kudin mai ne amma ba wai ita NNPC zata kara farashi ba. Yace ko a lokacin hutu kasar nada isasshen mai saboda haka babu wani dalilin kara farashin .

Dan kungiyar kwadago dake wani bangaren kungiyar ma'aikatan fetur Kwamred Nasiru Kabir yace da irin raderadin nan akan wayi gari da karin farashin litar mai. Yace haka kamfanin keyi. Yayi anfani da muryar mutane biyu. Idan wani ya fada dayan kuma ya fito ya karyata. Yace haka suka yi lokacin da zasu kara daga nera 87 zuwa nera 145 kuma aka wayi gari da karin.

Kwamred Kabir ya ja kunnen gwamnati yana cewar kada tayi kuskuren kara farashin mai saboda na baya da tayi talaka bai anfana ba. Ya kara da cewa sun yi nasu binciken sun kuma gano ana shirin kara kudin mai zuwa nera 200 lita daya.

Sai dai kakakin NNPC din Garba Deen Muhammad ya gargadi 'yan Najeriya da kada su damu da labarin da bashi da tushe.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG