Kuncin Rayuwa Ce Take Sa Mutane Ficewa daga Kasashensu

Yadda bakin haure ku fafutikar gujewa kasashensu

'Yan kasashen Afirka da yawa ne suke ratsawa ta hamada zuwa Algeria da Libya da nufin shiga nahiyar turai saboda kuncin rayuwa da suke fama dashi a nasu kasashen kuma sau tari mutane na mutuwa a hamada ko kuma su nutse a tekun baharum

A washegarin bayyanar labarin tsintuwar gawarwakin mutane 34 a arewacin jamhuriyar Nijer masu bin diddigin al’amuran da suka shafi tafiye tafiyen ‘yan ci ranin nahiyar Afirka sun bayyana cewa tsauraran matakan tsaron da aka dauka akan hanyar Agadez zuwa Algeria shine dalilin dake sanya bakin haure kokarin bullo da sabuwar barauniyar hanya. Saboda haka suka gargadi gwamnatocin kasashen Afirka ta yamm su kara matsa kaimi a ayyukan fadakarwa da samarda aikin yi don takaita wannan matsala dake daukar sabon salo a kulliyaumin.

Wakilinmu Muryar Amurka ya tantauna da SAIDU ABDU wani wanda ya gudanar da bincike akan dalilan yawaitar ‘yan ci ranin Afirka.

Ga cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kuncin Rayuwa Ce Take Sa Mutane Na ficewa daga Kasashensu - 3' 02"