Alhaji Farouk Aliu Mahama, dan tsohon mataimakin shugaban kasar Ghana mai rasuwa, ya ce akwai bukatar a gaggauta samar da dokar da zata kare auren Musulmi yadda ya kamata a kasar Ghana.
Yayin jawabinsa ya ce, “Mu na sa ran cewa gwamnati mai ci ko gwamnatin da za ta biyo bayanta za ta zo ta ba wa Musulmi dama, don mu tabbatar da cewa an zartar da kudurorin da ke da muhimmanci a gare mu kamar dokar aure da na saki. Kuma tare da goyon bayan Babban Limamin kasa da Mataimakin Shugaban kasa, za mu iya samun nasarar hakan.”
Ya kara da cewa "Kudirin Aure da Saki na da matukar muhimmanci duk da cewa Musulmi ba su karfafa kashe aure ba, kuma zan hada kai da shugabannin majalisa da ofishin babban mai shari'a don zartar da wannan kudiri."
Da yake tsokaci kan dokokin Ghana, Babban lauya kuma Malami a Jami’ar koyar da ilimin aikin jarida, Tanko Musa Zakariya, ya ce akwai kararrakin aure da yawa da kotu ba za ta iya saurara ba, idan babu takarda, musammam rabuwar aure ko rabon gado idan har Musulmi ya kai karar hakan a kotu.
Zakariya ya ce yana da muhimmanci idan an daura aure a masallaci aje ayi rajista da hukuma.
Anasa bangaren, Sheikh Haruna Abdul Hamid, wanda malami ne da ya kware a kan rabon gado, ya ce tun asali babu inda aka ce ayi aure ayi takarda ba, ya kara da cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya nuna abubuwan da in ba a yi su ko ba bu su ba aure, shine waliyi, da sadaki da shaidu da sauransu.
Ya kara da cewa, saboda yanayin rabuwar aure na zamani, idan ma za’a tabbatar da dokan kada ya taka dokar Addini Musulunci na aure.
Sai dai mafi yawancin jama’ar Ghana sun yi maraba da wannan kudirin, inda suka ce zai taimaka kwarai da gaske.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim:
Your browser doesn’t support HTML5