Magoya bayan shugaban kasar Gabon Ali Bango da babban abokin adawar sa Jean Ping, kowannen su na ikirarin samun nasara a zaben da aka gudanar a kasar, haka kuma suna cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa.
WASHINGTON, DC —
Yayin da Ping dan shekaru 73 da haihuwa ke cewa shine yayi nasara a zagayen farko na zaben, sai kuma a wuri daya mai magana da yawun shugaban Ali Bango yake cewa shugaba Bango ya dunfari samun nasara zagaye na biyu.
Idan dai har Ping ya samu nasarar zaben to wannan zai kawo karshen mulkin iyalan gidan marigayi Umar Bango.
Shi dai Ali ya gaji mahaifin sa ne Umar Bango, wanda ya rasu a shekarar 2009 bayan ya kwashe shekaru 41 yana mulkin kasar ta Gabon.
Gobe Talata ne dai ake sa ran fidda sakamakon zaben a hukumance.