Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Somaliya An Kawo Karshen Kawanyar da 'Yanbindiga Suka Yiwa Wani Gidan Cin Abinci


Harabar inda 'yanbindigan suka tada bam kafin su soma harbi
Harabar inda 'yanbindigan suka tada bam kafin su soma harbi

Jami’an tsaron Somaliya sun ce an kawo karshen wata mummunar kawanya da wasu ‘yan bindiga suka yiwa wani gidan cin abinci a babban birnin kasar, inda akalla mutane bakwai suka rasa rayukansu, ciki har da mahara biyu.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Mogadishu, Kanar Bishar, ya ce da sanyin safiyar yau Juma’a aka kawo karshen wannan kawanya.

Harin ya fara ne bayan da wata mota dauke da bam ta fashe a daren Alhamis, a kusa da gidan cin abincin Banadir, wanda aka biyo bayanshi da musayar wuta.

Tuni dai mayakan Kungiyar Al Shabab suka dauki alhakin kai wannan hari.

Kanar Bishar ya jaddada cewa, mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, ciki har da fararen hula biyar da wasu jami’an tsaro biyu.

Ya kuma ce an kashe mahara biyu yayin da aka cafke guda daga cikinsu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ga masu ba da agaji suna daukan gawarwakin mutane daga inda harin ya faru, da safiyar yau Juma’a

Har ila yau anga motar daukan majinyata ta dauku wasu mutane hudu da suka samu raunuka.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG