Jami’an ‘yan sanda sunce bom ya fashe a kofar gidan cin abinci dake wajen shakatawa na Banadir beach, kafin wasu ‘yan bindigar su ruga ciki da bude wuta.
Jami’an tsaron Samali sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar. ‘Daya daga cikin ‘yan sandan yace an harbe maharan, amma babu tabbacin cewa sun mutu ne baki ‘dayansu ko akwai masu rai.
A cikin watan Janairu ne kungiyar Al-Shabab ta kai hari wani otel dake makwabciyar Samalia, inda ta kashe mutane sama da 20.
Wakilin Muryar Amurka, Harun Maruf, ya aiko da rahotan tashin wani bom a jiya Alhamis, a wata kasuwar garin Bardhere dake kudancin Samali, wanda ya raunata mutane 12 ciki harda jami’an tsaro da kuma wani kwamishinan yankin.
Kungiyar Al-shabab mai alaka da al-Qaida, na kai hare haren ta’addanci a kokarinta na kassara gwamnatin Samalia. Ofishin ‘yan sandan da na jami’an tsaro da kuma guraren masu yawan shakatawa na daga cikin inda suke aunawa.