Shugaban kwamintin horaswa na hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya ce akwai iya yiwuwar sabon kocin kungiyar U20 Emmanuel Amonike ya maye gurbin babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh a sakamakon irin gagarumin namijin kokarin da yayi na jagorancin ‘yan kasa da shekaru 20 wajan samun nasarorin da dama.
Kwamitin zartaswa na hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ne ya karawa Amunike girma wajan bashi alhakin jan ragamar kungiyar Flying Eagles cikin wannan makon bayan lashe kofin duniya na hukumar FIFA a shekarar 2015 data gabata a kasar Chile.
Shugaban ya kara da cewa idan kocin ya ci gaba da bada kokari kamar yadda kungiyoyin da ya jagoranta suka nuna bajinta da kwarewa, babu shakka zai iya samun Karin girma domin jan ragamar babbar kungiyar ta kasa Super Eagles.
Barrister Green ya ce “idan Amunike ya yi kokari a wannan aikin da aka damka masa har kungiyar ta kaiga fitar da mu kunya a wasan cin kofin duniya, na yi imanin cewar kowa zai so a hanunta masa shugabacin babbar kungiyar, kuma lallai tana iya yiwuwa baza mu kawas da kai wajan tabbatar da yin hakan ba.”
Daga karshe shugaban ya yi kalaman kara hura wuta ga Koc Sunday Oliseh inda ya ce kodai ya kara zage damtse domin tabuka abin kirki kokuma ya ayi waje dashi.