Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kashe Makudan Kudade Wajen Rabuwar Aure A Kasashen Yammaci


Chechen Wedding
Chechen Wedding

A kowace kasa da yadda ake gudanar da mu’amalolin rayuwa, da ya banbanta da wata al’adar ta wata kasar. A mafi’akasarin kasashen yanmaci, suna da wata al’ada wadda idan mata da miji suna bukatar rabuwa, wato miji ya saki matar shi. Ba kawai mutun zai dauki takar da ya rubuta cewar ya saki matarshi shike nan ta saku ba.

A kasar Amurka idan mata da miji suka yarda da su rabu, to akwai bukatar su nemi lauya wanda zai rubuta takardar saki, kuma hakan zaisa sai sun biya lauyan makudan kudi. Babban dalilin da yasa suke haka shine, suna kokari wajen rage yawan sake-sake a tsakanin ma’aurata.

Daya daga cikin al’adar su shine, idan mata da miji su kayi aure sai mijin ya samu arziki duk suna tare, koda bayan wasu shekaru yana da bukatar su rabu, za’a dauki wani kaso na kudin shi a ba matar, don ta samu ta tallafama kanta kamin ta samu wani mijin ko kuma ta dai warware ciwon rabuwa.

Hakan yasa da dama suna tsoron rabuwa da matan su idan sunyi kudi. Kuma idan har da bukatar a yi sakin, to sai sun biya kudi da suna iya kaiwa daga dalla $15,000 zuwa $20,000 kwatankwacin naira milliyan uku N3,000,000 kamin lauya ya rubuta takardar saki a tsakanin su. Wadannan kudin suna danganta da yanayin gari da irin kudin mutun wasu ma suna wuce hakan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG