Kowa Yana Da Rawar Takawa Don Yakar Kalaman Batanci

  • Ladan Ayawa

TARABA: Taron zaman lafiya

Shugaban kungiyar bunkasa ci gaban fasahar sadarwa mai suna CITAD tace kowane dan Najeriya na da rawar da zai taka domin samar da zaman lafiya cikin kasa.

Shugaban na kungiyar ta bunkasa ci gaban fasahar sadarwa mai suna CITAD da ke bibiyar kalamun batancin da ake yayatawa a kafofin yada labarai da kuma na sada zumunta, yayi bayanin cewa kalamun batanci masu nasaba da addini da kabilanci sai karuwa suke yi a cikin al’umma.

Cibiyar tayi wannan bayanin ne a wani taron data gudanar a Bauchi na masu ruwa da tsaki musammam masu mu'amala da kafofin yada labarun da suka hada da ‘yan siyasa da kuma ‘yan jarida.

Jim kadan da kammala taron nasu, shugaban na CITAD Malam Zakariya Ya'u yace, kalaman batanci a cikin al’umma har yanzu da sauran rina a kaba. Ya shaidawa wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Abdulwahab Mohammed yadda yake kallon abin.

Inda yace sun lura cewa yaki da kalaman batanci da sauran hobbasar da ya kamata kowa yayi, don haka kowa yana da rawar da zai taka. Yace musamman a ‘yan kwanakin nan lamarin sai karuwa yake yi ta fuskar addini da kabilanci.

Ga Abdulwahab Mohammed da rahotonsa cikin murya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kowa Yana Da Rawar Takawa Don Yakar Kalaman Batanci - 3'53"