Gwamnati ta maida martani a ranar Talata a kan bukin rantsarwa, ta ayyana jam’iyar ‘yan adawa a matsayin kungiyar masu aikata laifi, ta kuma umarci gidajen telbijin su daina gabatar da shirye shiryen su.
A wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ya tabbatar da Uhuru Kenyatta zababben shugaban Kenya, yayin da sanarwar ke kuma nuna matukar damuwa akan matakin gwamnati na rufewa, da musgunawa da kuma hana kafafen yada labarai aiki.
An zabi Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban Kenya ne a ranar 26 ga watan Oktoban shekarar 2017, a cikin wani zabe da kotun kolin Kenya tayi na’am da shi, inji mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert a jiya Alhamis
Ta kara da cewa, wajibi ne abi hanyoyin shari’ar wurin warware kowace takaddama.
Babban kotun birnin Nairobi ta umarci gwamnati a jiya Alhamis ta ba manyan gidajen talabijin kasar su uku, daman fara aiki, bayan sun yi kokarin nuna hotunan bukin rantsar da Odinga.
Facebook Forum