Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Berom Sun Bukaci A Maida ‘Yan Gudun Hijira na Cikin Gida Garuruwansu


PLATEAU: Taron matasa Kirista da Musulmi
PLATEAU: Taron matasa Kirista da Musulmi

Kungiyar matasa kabilar Berom ta bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da ‘yan gudun hijira na cikin gida da suka kauracewa mahallansu, biyo bayan tashin hankalin da aka shafe shekaru ana fama da shi a jihar Plato.

A taron manema labarai da kungiyar ta kira ta bayyana cewa, dubban jama’a ne daga kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom ke gudun hijira, lamarin da ya sanya ‘ya’yansu shiga halin ha’ula’i.

Choji Dalyop, shugaban kungiyar matasan Berom ta kasa da kasa ya bayyana cewa, akwai mutane da yawa da rikincin ya tada su daga gidajensu, ya zama da dama basu iya komawa gida suyi noma. Wannan ya jefasu cikin matsananciyar wahala.

Yace sun kira taron manema labaran ne domin gabatar da damuwarsu. Bisa ga cewarsa suna da wurare guda hamsin da hudu da hargitsi yasa al’umar Berom suka kauracewa wuraren, yace wuraren da suke tsugune yanzu haka ya cunkushe ya kasa masu, ya kuma bayyana cewa, gwamnati tana da ‘yanci tasa mutanen su koma wurarensu.

A nashi jawabin, Barrister Dalyop Solomon daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar yace suna goyon bayan gwamnatin jihar Plato ta kafa dokar hana kiwo a fili. Ya bayyana cewa, satar shanun da ake yi , ba a ruga ake binsu a sace ba, ana sace su lokacin da aka fita dasu kiwo. Yace abinda zai taimaka wajen kawo karshen satar shanun shine a hana kiwo a fili wanda yake haifar da rikicin tsakanin manoma da makiyaya. Yace suna fargaban kada gwamnati tayi amfani da wuraren mutane da rikicin ya tilasa kaura wajen maida su wuraren kiwo.

Saurari Rahoton Zainab Babaji domin jin bayanin gwamnan jihar Plato Simon Lalong kan wannan batun

An yi kira ga gwamnatin tarayya ta maida 'yan gudun hijira garuruwansu-3:51"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG