Wani alkalin kotun tarayyar dake Legas a Najeriya, ya baiwa gwamnatin tarayya ikon ci gaba da rike naira miliyan 400 da hukumar EFCC ta gano a wani shagon mai hada-hadar kudaden waje dake tsibirin Victoria Island.
WASHINGTON D.C. —
Har ila yau, alkalin ya bai wa hukumar EFCC umurnin ta saka talla a wasu jaridun Najeriya da za ta kira duk wanda ya san kudin na shi ne ya taho kotu tare da shaidun mallakar makudan kudaden.
Alkalin ya ba da kwanaki 14 na cigiyar wanda ya mallaki kudaden idan kuma babu wanda ya fito fili bayan kwanaki goma sha hudun kotun za ta mallaka wa gwamnatin tarayya kudaden.
EFCC ce ta shigar da karar ta hannun Moses Awolusi wanda ya ce an samu kudaden ne a cikin wasu manyan jakankuna a wani shagon mai musayar kudaden waje duk da cewa an kwashe kusan shekaru biyu ba'a yi amfani da shagon ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5