A wani hukunci da ta yanke a yau Laraba 6 ga watan Satumba, Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta ce ba za a iya tilasta wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) fitar da sakamakon zabe ta hanyar na’urar yanar gizo ta Bvas ba.
Mai shari’a Haruna Tsammani, ya jaddada cewa INEC ce ke da hurumin tantance hanyar watsa sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kotun kuma ta yi tsokaci kan sashe na 52 da 65 na dokar zabe ta 2022 inda ta jaddada hurumin INEC na tsara yadda ake yada sakamakon zabe yayin gudanar da zabe.
Sakamakon haka, kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar Labour Party (LP) da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi suka shigar.
Jam’iyyar LP dai ta nemi a soke nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu daga jam’iyyar APC ne a bisa zargin gazawar hukumar ta watsa sakamakon zabe ta bututun bayanai na (IReV) wajen shigar da sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo.
- Yusuf Aminu