Kotun Najeriya Ta Wanke 'Yan Lebanon Uku Daga Ayyukan Ta'addanci, Amma

Hukumomin tsaron Najeriya sun damke Talal Roda da Abdallah Thahini da kuma Mustapha Fawaz.

Dayansu zai shafe tsawon rayuwarsa a kurkuku a saboda samunsa da laifin shigar da makamai Najeriya, yayin da kwararru ke cewa wannan hukumci koma-baya ne ga hukumar 'yan sandan ciki ta DSS
Jumma'ar nan wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeria ta wanke wasu mutane uku 'yan asalin kasar Lebanon da ake zaton 'yan kungiyar Hezbollah ne daga laifuffukan da aka tuhume su da aikatawa na ta'addanci, amma dayansu an same shi da laifin mallakar makamai kuma zai shafe tsawon rayuwarsa a kurkuku.

Hukumomin tsaron Najeriya sun damke Mustapha Fawaz da Abdallah Thahini da kuma Talal Roda a cikin watan Mayu, bayan da aka samu wasu makaman da aka boye karkashin wani gida a birnin Kano dake arewacin Najeriya.

An yi zargin cewa mutanen su na kulla makarkashiyar kai farmaki a kan wasu cibiyoyin kasashen yammaci da na Isra'ila ne a Najeriya, amma mutanen sun musanta da cewa wannan karya ce tsagwaronta.

Alkalin Babbar Kotun tarayya a Abuja, Adeniyi Adetokunbo Ademola, yace kungiyar Hezbollah ba kungiya ce ta ta'addanci ta kasa da kasa a idon dokokin Najeriya ba, saboda haka zamowa memba na wannan kungiya ba aikata laifi ba ne.

Alkalin yace babu wata shaidar da aka gabatar dake nuna cewa mutanen su na shirya kai hari, ko kuma sun samu horaswa na ta'addanci kamar yadda masu gabatar da kara suka yi zargi.

Haka kuma an sallami dukkan mutanen uku aka wanke su daga zargin batar da sawun kudaden haramun.

Sai dai kuma an samu Talal Roda da laifin makarkashiyar shigar da makamai zuwa cikin Najeriya, aka kuma yanke masa hukumcin daurin rai da rai.

Lauyan mutanen uku, Ahmed Raji, ya bayyana farin cikin cewa kotun ta yi watsi da dukkan manyan laifuffukan da aka tuhumi mutanen da aikatawa, yana mai cewa zai tuntubi Roda ko zai daukaka karar samunsa da laifin mallakar makamai da aka yi.

Daya daga cikin mutanen, Fawaz, yana da wani wurin shakatawa da ake kira Wonderland a Abuja, kuma kotun ta bayar da umurnin da a sake bude wannan wuri da hukumomi suka rufe bayan kama shi.

Nan take aka saki Fawaz da Thahini suka yi tafiyarsu zuwa gidajensu.

Wannan hukumcin wata babbar koma-baya ce ga hukumar 'yan sandan cikin Najeriya, DSS, wadda a watan Satumba ta yi ikirarin cewa 'yan Boko Haram sun kai farmaki kan sojoji a kofar wani ginin gwamnati a Abuja. Amma daga baya, sai shaida ta nuna cewa jami'an tsaro ne suka kai farmaki a kan wasu 'yan share wuri zauna.