Kotun Kolin Amurka Ta Haramta Amfani Da Tiktok

Hukuncin, wanda ya biyo bayan gargadin da gwamnatin Biden ta sha yi na cewwar manhajar ta na matukar barazana ga tsaron Amurka saboda alakarta da China, zai bada damar haramcin ya fara aiki a ranar Lahadi.

A yau juma’a kotun kolin ta yanke cewa haramcin da ta kakabawa dandalin na TikTok mai cike da cece-kuce zai fara aiki a karshen makon da muke ciki, inda ta yi watsi da rokon da mamallakan manhajar suka yi na cewa hakan ya sabawa dokar ‘yancin fadin albarkacin baki.

Kotun ta zartar da hukuncin da ba’a bayyana sunan alkalin da ya yanke shi ba sannan babu wanda ya nuna rashin yarda game da shi.

Hukuncin, wanda ya biyo bayan gargadin da gwamnatin Biden ta sha yi na cewwar manhajar ta na matukar barazana ga tsaron Amurka saboda alakarta da China, zai bada damar haramcin ya fara aiki a ranar Lahadi.

Kotun ta bayyana cewa Majalisar Dokokin Amurka ta maida hankali a kan matsalolin tsaron kasar, don haka hukuncin zai bata damar shigowa cikin lamarin.

“Majalisar ta yanke cewa ya zama wajibi a cefanar da dandalin domin magance damuwar da take dashi a kan tsaron kasar game da dabi’ar TikTok ta tattara bayanan sirri da kuma alakarsa da wata abokiyar gaba a ketare,” kamar yadda kotun ta wallafa.