Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar da dan takarar shugaban kasa karkashin Inuwar Jam’iyyar PDP yayi na gabatar da sabbin hujojji a gaban ta.
abuja, najeriya —
Kotun kolin ta bayana hakan ne a yayin zaman sauraron karar a ranar Alhamis, inda ta ce karbar sabbin hujojji ya sabawa kundin tsarin mülkin kaşar na shekarar 1999 kamar yadda aka yi mata garambawul.
Kotun ta kalubalanci jam’iyyar PDP a kan me ya hana ta mika sabbin hujojjin a cikin wa’adin kwanakin da doka ta tanadar, kama daga kwanakin shigar da kara 21 zuwa kwanaki 190 na sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
A cewar kotun, kamata ya yi jam’iyyar PDP ta shigar da kara a kan zargin takardun bogi tun shekarar 2022 zuwa watan Maris na shekarar 2023.
Ta kara da cewa ba za ta saurari bukatun kara duk wasu korafe-korafe ko shaidu da ba’a gabatar wa kananan kotunan baya ba.