Kimanin sojoji 22 ne zasu gurfana a yayin shari’ar da za a shafe kwanaki 5 ana gudanarwa a wannan zama dake matsayin na farko a shekarar nan ta 2020. Ana zargin wasu daga cikin wadanan sojoji da laifin tserewa daga fagen daga a yayin kafsawa da abokan gaba, sai rukuni na 2 na wadanda ake tuhuma da satar bindigogi da albarusai sannan sai shari’ar zargin aikata kisan kai da gangan da wace ta shafi zargin amfani da takardun bogi, kamar yadda kwamishina mai kare muradun gwamnatin Nijer, General Abou Tarka ya bayyana a yayin soma zaman kotun.
To ko yaya jami’an kare hakkin dan adam ke kallon wannan yunkuri? Kamar sauran masu bayyana ra'ayi, Abdou Elhadji Idi na gamayyar kungiyoyin FSCN na mai fatan ganin an gudanar da wannan shari’a a karkashin doka.
A bisa tsarin dokokin shari’a a nan Nijer, Kotun hukunta laifukan Soja na daga cikin jerin kotunan dake karkashin kotun karya shari’a saboda haka doka ta bada damar daukaka kara a duk lokacin da mutun ya ga alamar ba a yi masa adalci ba: ma’ana zancen rashin adalci ya kau a kotun ta tribunal Militaire inji shugabanta Mai Shari’a Alio Daouda.
Da dama daga cikin ‘yan kasa sun yi zaton zaman kotun na wannan karon zai tabo shari’ar Kanar Soumana Zanguina da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnati da wata shari’ar da ta shafi kisan matashin hafsan nan matukin jirgin sama, Chamsoudine Tchombianoda wanda ya mutu a watan Disamban 2018, lokacin da yake karatu a makarantar horon soja dake Tondibia to, amma mai kare muradun gwamnati yace tuntuni maganar ke hannun wata kotun ta daban .
Saurara cikakken rahoton Souley Barma a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5