Alkalan kotun hukunta laifuffukan yaki ta kasa da kasa (ICC) sun bada sammacin kama firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministn tsaronsa, da shugaban kungiyar Hamas, Ibrahim Al-Masri, akan zargin aikata laifuffukan yaki da cin zarafin bil adama.
washington dc —
Hakan na zuwa ne bayan da mai shigar da kara a kotun Karim Khan ya bayyana a ranar 20 ga watan Mayun da ya gabata cewa yana neman sammaci a kan zargin aikata laifuffukan dake da nasaba da harin da kungiyar Hamas ta kaiwa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da kuma martanin da rundunar sojin Isra’ila ta mayar a Gaza.
ICC tace ba’a bukatar Isra’ila ta amince da hurumin kotun.
Isra’ila ta ki amincewa da halascin kotun dake da mazauni a birnin Hague sannan ta musanta zargin aikata laifuffukan yaki a Gaza.
Isra’ila ta yi ikirarin hallaka Al-Masri, da aka sani da Muhammad Deif, a wani hari ta sama sai dai Hamas bata tabbatar ko musanta hakan ba.