Kotun daukaka karar ta bayyana cewa, janye yajin aikin shine kawai sharadin da kungiyar ke bukata don neman daukaka karar hukuncin kotun ma’aikata.
Sai dai kotun ta amince da bukatar ne bisa sharadin cewa, kungiyar ta yi biyayya ga hukuncin da karamar kotun ta yanke, sannan kuma ta janye yajin aikin nan take har sai an yanke hukunci.
Kotun ta baiwa kungiyar ASUU wa’adin kwanaki bakwai da ta shigar da kara a cikinta biyo bayan bin hukuncin da karamar kotu ta yanke.
Sai dai ci gaba da sauraron karar jiya Alhamis, lauyan kungiyar ASUU, Femi Falana (SAN), ya shaida wa kotun daukaka kara cewa bangarorin biyu ba za su iya warware yajin aikin da aka shafe watanni takwas ana yi ba a wajen kotu.
James Igwe, lauyan gwamnatin tarayya, ya kuma shaidawa kotun daukaka kara cewa duk shawarar da aka basu, sun kasa warware takardamar.
A hukuncin da ya yanke yau Jumma’a, alkalin kotun, Mai shari’a Hamma Barka, ya umarci malaman da su koma bakin aiki cikin gaggawa.