An kama Meng ne a filin saukar jiragen sama a birnin Vancouver bisa ga sammacin kamota da Amurka ta bayar a kan zarginta da take dokokin takunkumin kasuwanci da Iran
Alkali William Ehrcke ya bada belinta a kan kudi dala miliyan bakwai da dubu dari biyar tare da gindaya sharudda a kan Meng. Sharuddan sun ce zata ci gaba da zama a gundumar British Columbia a can Canada, a cikin gidan da mijinta ya mallaka kuma ba zata fita gida daga karfe 11 na dare zuwa karfe shida na safe ba. Za a kuma sanya ido a kan Meng a ko da yaushe.
Meng itace babbar jami’ar kudi a katamfaren kamfanin fasahar sadarwar China na Huawei, da mahaifinta ya kafa kuma yana cikin manyan kamfanonin dake kera wayoyin hannu a duniya. Iyalanta suna da dukiya da ta kai biliyoyin daloli.
A halin da ake ciki kuma, China ta kama tsohon jakadar Canada a China Michael Kovrig a kan wasu dalilai da basu bayyana ba.