Kotu Tayi Watsi da Karar 'Yan Adawa A Zambia

Masu goyon bayan shugaban kasar Zambia Edgar Lungu

Shugaban ‘yan adawan kasar Zambia yace hukuncin farko da mai shara’a ya bayar yasa ya gaza cimma damar kalubalantar sakamakon zaben na 11 ga watan Agusta.

A jiya Littini ne dai kotu tayi watsi da karar da dan adawar ya shigar. Ukku daga cikin Alkalai biyar sun yanke hukuncin cewa kwanaki 14 da aka bayar domin sauraren kukan mai karar ya kawo karshe daga tsakiyar daren ranar biyu ga watan Satumba.

Jamiyyar United Party For Development (UPND) tace kotun tayi amai ta lashe, domin ko tace mai shara’a Ann Mwewa-Sitali tace zata saurari kukanta daga 2 zuwa 8 ga watan Satumba.

Amma kuma daga baya sai alkaliyar da kanta ta dawo tana cewa tayi kuskure a hukuncin da ta yanke cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.Inji Conelius Mweetwa dan majilisar dokokin kasar kuma mukaddashin mai magana da yawun jamiyyar ta UPND shine ya shaidawa Muryar Amurka hakan.

Yace daga yanzu mun gane cewa mu muna cikin wata Zambia ce ta daban, wato muna cikin wadda bata bin doka da oda.