Wata kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta yankewa Hon. Farouk Lawal hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekara bakwai.
Lawal shi ne tsohon shugaban kwamiti a Majalisar wakilai da ke sa ido kan harkar kudaden tallafin mai a Najeriya.
Wannan hukunci na zuwa ne, bayan da kotun ta same shi da laifin neman cin hancin dala miliyan uku daga wajen hamshakin mai kudin nan Femi Otedola, a lokacin ana bincike kan kudaden tallafin mai a shekarar 2012.
Karin bayani akan: Farouk Lawal, Goodluck Jonathan, Daily Trust, Channels, Nigeria, da Najeriya.
Lamarin dai ya faru ne a zamanin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.
Mai Shari’a Justice Angella Otaluka ce ta yankewa Lawal Hukuncin, bayan da aka tuhume shi da aikata laifuka uku, kamar yadda kafafen yada labaran kasar da dama da suka hada da Daily Trust da Channels suka ruwaito.
Bayanai sun yi nuni da cewa, tsohon dan majalisar ya nemi Otedola ya ba shi cin hanci don ya soke sunan kamfaninsa daga jerin kamafanonin da ake zargi da badakala a fannin kudaden tallafin na mai, zargin da ya sha musantawa.