Kotu Ta Yanke Wa 'Yan Jarida Hukuncin Dauri A Gidan Yari Saboda Sukar Gwamnatin Tunisiya

Mourad Zeghidi are set to appear in court on May 22, 2024.

Bsaïs da Zeghidi sun musanta zargin. Dukkansu sun ce suna gudanar da ayyukansu ne kawai, wajen nazari da sharhi kan ci gaban siyasa da tattalin arziki a Tunisiya.

A ranar Larabar da ta gabata ne wata kotu a kasar Tunisiya ta yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso ga wasu 'yan jarida biyu na gidan talabijin da rediyo saboda sukar gwamnati kan shirye-shiryensu da kuma shafukan sada zumunta.

Yan uwan Mourad Zghidi

An daure Borhane Bsaïs da Mourad Zeghidi kowannen su gidan yari na tsawon watanni shida saboda yada "labaran bogi" da kuma karin watanni shida saboda "yin maganganun karya da nufin bata sunan wasu," wato shugaban Tunisiya Kaïs Saied, in ji kakakin kotun Mohamed Zitouna.

TUNISIA-MEDIA-TRIAL-RIGHTS-POLITICS

Hukuncin ya zo ne kasa da makonni biyu da kama su.

Suna cikin manyan gungun 'yan jarida, masu fafutuka da lauyoyi da ake tuhuma a karkashin dokar ta 54, dokar da ta haramta yada "labaran karya" da nufin cutar da lafiyar jama'a ko tsaron kasa.

Dokar da aka amince da ita a shekarar 2022 don yaki da aikata laifuka ta yanar gizo, ta sha suka sosai daga masu fafutukar kare hakkin bil adama wadanda suka ce ba a fayyace laifuffukan ba a fili kuma ana amfani da su wajen murkushe masu sukar shugaban.

Bsaïs da Zeghidi sun musanta zargin, inda suka ce suna gudanar da ayyukansu ne kawai, wajen nazari da sharhi kan ci gaban siyasa da tattalin arziki a Tunisia.

Shari'ar dai ta fuskanci suka daga kasashen duniya tare da janyo suka a kasar Tunisia, inda 'yan jarida da dama suka hallara a gaban kotun domin nuna goyon baya.