Kotun wacce ke karkashin jagorancin mai shari'a Adebukola Banjoko ta sami tsohon gwamnan da laifi dumu dumu na zamba cikin aminci na zunzurutun kudi har Naira Biliyan daya da miliyan sittin da hudu a karar da hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya wato EFCC ta gabatar.
Mr Jolly Nyame wanda ya jagorancin jihar Taraba daga 1999 zuwa 2007 an tuhumeshi da laifukan zamba cikin amici da ha'inci da cin amana da babakere da dukiyar jama'a dama karin wasu tuhume tuhume har 41 inda kotun ta tabbatar masa da laifukan 27 wadda kuma ta tura shi gidan wakafi.
Bisa yadda aka yanke hukuncin, tsohon gwamnan Nyame na da ikon daga ‘kara zuwa kotun daukaka ‘kara harma zuwa ga kotun koli in bai yarda da hukuncin kotun ba.